Iyalan Joe Biden | |
---|---|
iyali | |
Bayanai | |
Sunan dangi | Biden |
Significant person (en) | Joe Biden |
Joe Biden, shugaban Amurka na 46 kuma na yanzu, yana da 'yan uwa da suka yi fice a fannin shari'a, ilimi, fafutuka da siyasa. Iyalin Biden sun zama dangin farko na Amurka a bikin rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu, shekara ta 2021. Iyalinsa na kusa shine kuma dangi na biyu na Amurka daga 2009 zuwa shekara ta 2017,lokacin da Biden ya kasance mataimakin shugaban kasa. Kamar yadda zuriyar duk shugaban Amurikadayane, dangin Biden galibi zuriyar tsibirin Birtaniyane, tare da yawancin kakanninsu sun fito daga Ireland da Ingila, yayin da kuma suke da'awar zuriyar Faransanci. [1] [2]
Daga cikin kakannin kakanni goma sha shida na Joe Biden, goma an haife su a Ireland. Ya fito ne daga Blewitts na mayo da Finnegans na County Louth . [3] An haifi ɗaya daga cikin manyan kakannin Biden aSussex Ingila, kuma ya yi hijira zuwa Maryland a Amurka a cikin ko kafin 1822. [4]